On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gabanin Karewar Shekarar 2022 Za'a Sauyawa Wasu Takardun Kudi Fasali A Najeriya - CBN

Babban bankin Najeriya CBN yace zai sauya fasalin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1000

 

Gwamnan babban bankin kasar na CBN Godwin Emefiele shi ne ya bayyana hakan a ranar laraba yayin ganawa da manema labara a Abuja.

Yace  za’a sabunta kudaden ne daga ranar 15 ga watan Disamba na 2022.

Yayinda ya shawarci 'yan Najeriya su maida tsofin takardun naira da sauyin zai shafa ga bankuna domin  karbar sabbin kudaden, Emefiele ya ce an dauki matakin yin hakan ne da nufin samun cikakken iko akan kudaden da ake amfani da su a kasar.

Haka kuma,  yace akasarin kudaden suna yawo a hannun mutane wanda ba za'a lamunci hakan ba.

Emefele ya kara da cewa  kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen Najeriya ana hada-hada da su ne ba ta hanyar bankin ba.