On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula A Jihar Kano Sun Sha Alwashin Dakile Yunkurin Gwamna Ganduje Na Ciyo Bashin Naira Billiyan 10 Domin Sanya Kyamarorin Tsaro na CCTV

Kungiyoyin Fararen Hula A Jihar Kano Sun Sha Alwashin Dakile Yunkurin Gwamna Ganduje Na Ciyo Bashin Naira Billiyan 10 Domin Sanya Kyamarorin Tsaro Na CCTV

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Ibrahim A Waiyya Shine Ya yi Wannan Alwashi Ta Cikin Wani Sakon Murya Da ya Aikowa Arewa Radio Ranar Alhamis.

Idan ba'a manta ba a Ranar Laraba  Majalissar dokokin jihar Kano ta Salahewa gwamna Ganduje ya karbo Rancen Naira billiyan 10 Domin Sanya Na'urorin Tsaro na CCTV a Kwaryar birnin da Shalkwatar Masarautun Kano.

Sai dai kungiyoyin Fararen hular sunyi Allah wadai da wannan Yunkuri, suma masu mamakin yadda Majalissa ta sahalewa gwamna Ganduje wannan bukata.

Shugaban Kungiyoyin Waiyya, yace a yanzu bashin da ake bin jihar Kano ya Kai billiyan 175 Saboda haka wane Zai biya wannan bashi da ke karawa Mutanen jihar Nauyi.

Koda yake yace kungiyoyin ba sa adawa da duk wani yunkuri na Inganta tsaro, kuma sun jima suna marawa ayyukan tsaro ba ya.

Daga nan yace zasu Yi duk Mai yiwuwa wajen dakile irin wannan Yunkuri.

Ita kuwa Jam'iyyar hamayya PDP ta bakin Kakakinya Bashir Sanata,  ta zargi gwamnatin da yunkurin Barnar da dukiya tare da yin watsi da alhakin da ya rataya a wuyanya na bada Ilimi da Sana'oi ga Matasa.