On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gambari Ya Mika Ragamar Aiki Ga Gbajabiamila Amatsayin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Najeriya

Shugaban ma’aikatan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ibrahim Gambari, ya mikawa kakakin majalisar wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, ragamar aiki.

Gambari ya rike mukamin daga 2020 zuwa 2023 bayan rasuwar magabacinsa Abba Kyari a watan Afrilun 2020.

Yayin zaman wanda aka gabatar da takardar mika mulki ya gudana ne a jiya a fadar shugaban kasa da ke Abuja kuma shugaban kasa Bola Tinubu ya samu halarta.

A makon da ya gabata ne Tinubu ya bayyana nadin Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadarsa, yayin da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa ne aka nada shi a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.