On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ganduje Ya Kalubalanci Jam'iyyun Hamayya Su Gabatar Da 'Yan Takararsu Idan Suna Da Nagartar Kamar Na APC

Gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Kano.

 

Ganduje, yayin da yake jawabi a garin Gaya inda aka kaddamar da yakin neman zaben, ya bigi kirjin cewa jam’iyyarsa za ta kai ga samun nasara a dukkan matakai da ta ke fitar da ‘yan takara.

Ya ce dukkan ’yan takarar jam’iyyar sun cancanta yayin da yake kalubalantar jam’iyyun adawa da su gabatar da ‘yan  takararsu domin ganin ko za su iya tsayawa takara da ‘yan jam’iyyar APC.

Haka kuma Ganduje, ya bayyana karin kashi 50 cikin 100 na tallafin karatu ga daliban makarantun gaba da sakandare dubu 4.

Ya ba da umarnin a ba da tallafin Naira miliyan 100 ga dalibai dubu 4 na masarautar Gaya.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta bada fifiko ga ilimi mai inganci. Sai dai ya kalubalanci wadanda suka amfana da su ci gaba da maida hankali akan karatunsu na a fannoni daban-daban.

 

 

 

More from Labarai