On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ganduje Ya ce Sai Da Kamun 'Kafa Mataimaka Ke Kaucewa Fadawa Tarkon 'Yan Bani Na Iya

GWAMNA GANDUJE

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce mataimaka a kasar nan, dole ne su kasance masu yin kamun kafa da biyayya ga Iyayen gidansu idan har suna son tsira daga fadawa cikin tarkon wasu ‘yan bani na iya da kuma kaucewa tashin ‘yan kunji-kunji nan da can.

Ganduje ya bayyana haka ne a yayin  kaddamar da wani sabon  littafinsa mai suna, Tafiyar da harkokin Mataimaki da kuma jagoranci a Najeriya  wanda aka yi  ranar Talata a Abuja.

Ya ce littafin, wanda ya bada bayanin yadda  ya  fahimci abubuwan da suke wakana a kasar nan, yana daya daga  cikin abunda  ya shafi  rayuwarsa a aikin gwamnati.

A cewarsa, tarihin dangantakar da ke tsakanin wasu Gwamnoni da mataimakansu a kasar nan  tun a Jamhuriyya ta farko ta kasance ta rashin aminci da hassada da  kuma  cin amana.

Ya ce irin wannan matsaloli su temaka wajen raba kan jihohi da dama a shekarun  da suka gabata,  tare da yin illa ga ci gaban mutanen da suka zabi mutanen  domin jan ragamar  aiyukansu na gwamnati.

Gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje.

To sai dai kuma a yayin da  gwamna  Ganduje ke bayar da shawara  ga mtaimakan gwamnoni akan su kasance masu  biyayya, Shi kuwa  tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan  kira yayi da a samar da doka da zata kare mataimakan gwamnoni daga tsige su daga kan kujerunsu ba bisa ka’ida ba.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin da gwamna  Ganduje ya rubuta da hannunsa, Jonathan ya ce ya kamata ka’idojin da doka ta tanada su sanya mataimakan gwamnoni su kasance masu samun cikakken tsaro domin gudanar da aiyukansu batare da wani shayi ba.

Tsohon shugaban kasar, wanda shi ne shugaban taron, ya ce kamata ya yi a samar da tsarin doka domin faiyace irin aiyukan da suka wajaba a kan wuyan mataimakan gwamnoni , a maimakon dorasu kan wasu aiyuka na wucin gadi.

A cewarsa, matakin zai rage zaman dar-dar da ake samu a bangaren  harkokin gudanar da mulki.

Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa, Good Luck Jonathan.