On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Ganduje Zaisa Hannu Kan Hukuncin Kisan Da Aka Yiwa AbdulJabbar

Ganduje da Abduljabbar

Babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, Barrister Lawan Musa, Ya ce gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a shirye yake ya saka hannu kan hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yankewa, sheik Abduljabbar Nasiru Kabara.

Wata babbar kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ce  ta yanke  Abduljabbar Nasir Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, a saboda  yin kalaman batanci ga annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasalam.

Da yake tsokaci akan hukuncin, Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Ya ce a kowane lokaci gwamna Ganduje  na kokarin cewar  ba a karya doka da oda a jihar nan ba.

Ya kara da cewa akwai matakai da dama da ake bi kafin saka hannu kan dokar hukuncin kisa, kuma gwamnan a shirye yake ya saka hannu kan hukuncin kisan, da zarar an gabatar masa dashi.

A jiya ne, Mai shari’ar bayan ya yanke masa hukuncin kisa ya kuma bada umarni rufe masallatan sa guda biyu dake filin mushe da kuma wanda ke unguwar Sabuwar Gandu a nan Kano, sa’an nan kuma gwamnati zata kai littafan sa dakin karatu na jihar Kano.