On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Garin Daura Na Shirye-Shiryen Bukukuwan Tarbar Shugaba Buhari Bayan Karewar Wa'adin Mulki

Garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin shiri yayin da mazauna garin ke jiran tarbar dansu wanda wa'adinsa na shekaru takwas zai kare a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Mai martaba sakin Daura Dr Umar Farouq Umar, shine ke jagorantar shirye-shiryen bikin maraba da Buhari, wanda aka gani a karshen mako yana duba yadda shirye-shiryen ke gudana.

Domin tarbar shugaban, Masarautar Daura na shirya gagarumin hawan Dabar don karrama Muhammadu Buhari, da sauran al'adun gargajiya kamar dambe da kokawa da Shadi.

Sarkin ne ya fara ba da labarin shirin Dabar a lokacin da Gwamna Aminu Masari ya kai masa ziyarar bankwana a fadar sa a makon jiya.

More from Labarai