On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gobara Ta Cinye Wasu Injinan Cirar Kudi Guda Ukku A Nan Kano.

Bankin zenith

Wadansu Injinan cirar kudi na ATM dake bankin Zenith a akan Titin Tafawa Balewa dake cikin karamar Hukumar Nasarawa a nan jihar Kano,sun kama da wuta a Jiya.

Mai magana da yawun  hukumar kashe  gobara  ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ne ya  tabbatar  da haka ta  cikin wata sanarwa  da   ya fitar .

Ya kara da cewar  sun samu kiran neman daukin gaggawa   ta karfe 12 da mintina 6 na  tsakar ranar jiya,wanda  hakan yasa  suka yi gaggawar  daukar  mataki.

Kakakin hukumar kashe gobara  ta jihar Kano, Ya  ce Injinan  cirar kudi na ATM  guda ukku ne  gobarar  ta  cinye, A  yayin da wasu  guda  ukku  kuma suka ‘dan  tabu, inda  ya alakanta  tashin gobarar  da  matsalar  lantarki da aka samu a cikin injinan cirar  kudi  na ATM din.