On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gobara Ta Tashi A Ofishin Shirya Jarabawar WAEC Na Najeriya

ofishin WAEC

Hukumar Shirya jarabawar Kammala Makarantun Sakandire ta yammacin Afrika, WAEC, ta bawa jama’a tabbacin cewa dukkanin wasu muhimman bayanai dake cikin ofishinta na nan daram , babu abunda ya same su, bayan da wata Gobara ta tashi a ofishin hukumar dake Yaba a birnin ikko da safiyar yau.

Kazalika rahotanni sun baiyana cewa babu wani asarar rai da aka samu a sakamakon gobarar.

Sanarwar da shugaban  sashin hulda  da jama’a  na Hukumar,  Moyosola Adesina, ya godewa  Hukumar Kashe gobara ta jihar Legas da sauran hukumomin bada agajin gaggawa  game da gudunmuwar da suka bayar  kan lokaci.