On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamna Chukwuma Soludo Yace Peter Obi Wasan Kwaikwayo Yake Ba Takarar Shugaban Kasa Ba.

CHUKWUMA SOLUDO

Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya ce Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi shi da kansa ya san cewar ba zai ci zaben shugaban kasa mai zuwa ba.

Yayi ikirarin cewa jam’iyyar ta APC, kawai tana yin wasa ne, Tsohon gwamnan babban bankin kasar, sanann kuma gwamna a halin yanzu, Yace  wasan da Peter Obi ke yi shine babban dalilin da yasa yaki komawa jam’iyyar APGA.

Ya kara da cewa magana ta gaskiya mutane biyu sune ke takarar shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa, a yayin da sauran ke wasan kwaikwayo.

More from Labarai