On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Gwamna Ganduje Ya La'anci Jam'iyyun Adawa Dake Goyon Bayan CBN Kan Chanjin Kudi

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya la'anci jam'iyyun hamayya dakegoyon bayan tsarin chanjin kudi na babban bankin Najeriya CBN, inda ya bayyana wahalhalu da ake fuskanta a halin yanzu da Annobar CVID-23

Ganduje ya bayyana haka ne  jiya a fadar gwamnati yayin kaddamar da rabon kayan agajin domin saukaka wahalhalu da ake ciki.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya kara da cewa, abin da PDP da NNPP suke so shi ne mutane su ci gaba da kasancewa  cikin talauci,.

Ganduje ya ce, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin cewa idan aka zabe shi a zabe mai zuwa zai tabbatar ya kawo karshen wahalhalun da ake fuskanta sanadiyar tsare-tsaren  CBN 

Dangane da rabon kayan abinci, gwamnan ya ce,  ya raba kayan agajin ne domin rage tasirin wahalhalun da ke kawo matsala ga  rayuwar ‘yan Najeriya.

Da yake bayyana damuwa da cewa, wannan yanayin ba gwamnoni ko al'ummane suka roka ba, saboda  haka ba sa maraba da shi kwata-kwata. 

"A yau ’yan kasa na fuskantar matsalar COVID-23 da CBN ke haddasawa inji Ganduje

Da yake bayyana cewa, halin da akec ciki ya zama tamkara kwayar cutar da ta fitowa daga bankin CBN ta shafi dukkan bankunan kasuwanci da POS da  na’urorin ATM da duk wani abu da ke da alaka, ya ce  kasancewar jihar Kano da ta fi yawan al’umma a kasar nan, wannan yanayi mara dadi ya fi shafe su.

Ya yi nuni da cewa, wadanda zasu ci gajiyar tallafin sun fito ne daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano.