On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamna Ganduje Ya Tsaida Ranar Bude Kebantacciyar Kasuwar Magani Ta Kanawa

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana kudirin gwamnatinsa na yaki da jabun magunguna da haramtattu da marasa inganci da kuma miyagun kwayoyi a jihar Kano, yayinda  ya sanya ranar 10 ga watan Fabrairu na shekarar 2023 a matsayin ranar kaddamarwa da bude kebantaciyar sabuwar  kasuwar  magunguna ta Kanawa.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a wata ziyarar aiki da ya kai da masu ruwa da tsaki zuwa kasuwar da ke ‘Dangwauro kan titin zuwa Zaria, ya ce gwamnatinsa ta damu matuka da matsalar shan miyagun kwayoyi da sayar da magungunan jabu da marasa inganci saboda haka ya himmatu wajen tallafa wa gwamnatin tarayya kan shirinta na yaki da matsalar harkokin magunguna da ke sanadiyar asarar rayukan miliyoyin mutane a kasarnan.

Ya kara da cewa, idan aka kaddamar da kasuwar, ba za a sake barin wani wurin sayar da magani a sauran kasuwanni ba.Insert.

Da yake jawabi tun da farko, magatakardan hukumar kula da harkokin  magunguna ta kasa PCN, Pharmacist Ibrahim Babashehu Ahamed, ya bukaci masu samar da kasuwar da su gina katanga ba tare da bata lokaci ba domin su cika ka’ida da dokokin masana’antar harkokin magunguna yayin da ya gode wa gwamnan jihar bisa goyon bayan da yake bayarwa ga aikin.

A nasa bangaren, shugaban kasuwar magani ta Kanawa, Alhaji Hussaini Labaran Zakari, ya bayar da shawarar sanyawa kasuwar sunan gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje, yayin da ya yi kira ga dillalan magunguna da su yi biyayya ga manufofin gwamnati don amfanin kansu da al’ummarsu baki daya.