On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamna Inuwa Na Jihar Gombe Ya Nada Yakubu Kwairanga Amatsayin Sabon Sarkin Funakaye

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da nadin Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon Sarkin Funakaye.

Nadin na kunshe ne a wata wasika mai dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo.

Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnatin jihar Gombe Ismaila Uba ya fitar a ranar Litinin, ta tabbatar da nadin.

Sanarwar ta kuma ba da tabbacin gwamnatin gwamna Yahaya wajen ci gaba da baiwa masarautun gargajiya girmamawa ta musamman ganin irin rawar da sike  takawa wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kan al’umma.

Idan za’a iya tunawa a watan Agusta na shekarar 2022 Allah ya yiwa sakin Funakaye Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga na III yana da shekara 45.

 

More from Labarai