On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamna Kayode Na Jihar Ekiti Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Afrika

GWAMNA KAYODE FAYEMI

An zabi gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Afrika.

Ta cikin wata sanarwa da Babban sakataren yada labaransa, Yinka Oyebode ya fitar, ya baiyana cewa an kuma zabi Umar usman gwamnan arewacin kasar Kamaru a matsayin mataimakin shugaban kungiyar daga yankin Afrika ta tsakiya, sai Farfesa Peter Anyang wanda ya kasance gwamnan Kisumu daga kasar Kenya a matsayin mataimakin shugaban kungiyar  daga yankin Afrika ta Gabas.

Kazalika an zabi Mme Bouida Mbarka a matsayin mataimakin daga Arewacin Afrika  sai kuma David Makhura  shima a matsayin mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin afrika daga yankin kudancin Afrika.

Gwamna Fayemi wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnoni ta kasa ya lashi takobin yin amfani da damarsa wajen daga likafar nahiyar afrika ta hanyar yin amfani da muradan da kungiyar hadin kan afrika ta sanya a gaba, wanda zata yi aiki dasu har nan da shekarar 2063.