On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamna Masari Ya Zubar Da Hawaye A Zauren Majalissar Dokokin Jahar Katsina

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya zubar da hawaye a lokacin da yake gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2023 wanda ya kasance na karshe a wa’adin mulkinsa ga majalisar dokokin jihar.

Kasafin kudin wanda ya kai Naira biliyan 288 da milliyan 63, inda aka ware kashi 63.77 a matsayin na manyan ayyuka da kuma kashi 36.23 na tafiyar harkokin  yau da kullum.

Babu wata masaniya kan dalilin zubar da hawayen  gwamnan  amma hakan ya zo ne a lokacin da yake bayanin cewa a jimillar kasafin kudin ya yi kasa da na kasafin 2022 da aka sake  bibiya  da kusan Naira biliyan 34.

Ya bayyana cewa an tsara kasafin ne domin kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma fara wasu manyan ayyuka da za a iya kammala su a cikin ragowar wa’adin gwamnatinsa.

 

''Ya ce, “Kamar yadda ku ka sani, wannan shi ne karo na karshe da zan tsaya a gaban masu girma ƴan majalisar dokokin jihar Katsina domin gabatar da daftarin kasafin kudin gwamnatin jihar Katsina,”

Gwamnan, wanda ya fara da yin bita akan  kasafin kudin shekarar 2022 da muke bankwana da ita, ya kuma godewa 'yan majalissar da sarakunan gargajiya da sauaran al'umma bisa hadin kai da goyon baya da suka bayar wajen samun cigaban Jahar.

More from Labarai