On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamna Nyesom Wike Ya Kauracewa Taron Wadanda Suka Yi Takarar Shugaban Kasa A PDP Da Atiku Ya Kirawo

ATIKU DA GWAMNA WIKE

Gwaman Nyesom Wike na jihar Ribas bai halarci ganawar da Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben mai zuwa, Atiku Abubakar yayi da wadanda suka nemi takarar shugaban kasa tare dashi a cikin jam’iyyar a gidansa dake Asokoro a Abuja.

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da Dele Momodu a Mohammed Hayatu Deen  da Tari Oliver da kuma Charles Ugwu.

Atiku ya yaba masu bisa yadda suka karbi sakamakon zaben fidda gwanin wanda ya bashi nasarar zama dan takara, batare kuma da sun tada wata ‘kura ba.

Yayi alkawarin yin tare dasu gabanin babban zabe mai zuwa, inda ya baiyana cewa suna da rawar da zasu taka domin samun nasararsa a zaben mai zuwa.