On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamna Nyesom Wike Yace Ya Zama Dole Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Ya sauka Daga Kan Kujerarsa

SHUGABAN JAM'IYYAR PDP NA KASA DA GWAMNA WIKE NA JIHAR RIBAS

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya dage cewar dole ne sai shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa.

Wike ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shaida masa da kansa lokacin da ya lashe zaben fidda gwani a watan Mayu, cewa dole Ayu  ya sauka daga kan shugabancin jam’iyyar.

Gwamnan ya ce murabus din da sanata  Walid Jibril  yayi a  matsayin shugaban kwamitin amintattu ba zai dakatar da bukatarsa ​​na tsige sanata  Ayu daga kan shugabancin jam’iyyar.

A cewar gwamna  Wike, batun da ke gabansa a halin yanzu shine  tabbatar da adalci da kuma gaskiya , yana mai cewa kasancewar  yankin Arewcin kasar nan ya  samar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, bai kamata  yankin ya cigaba da rike shugabancin jam’iyyar ba.

Hakan na zuwa ne a yayin da, Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar  PDP, Sanata  Walid Jibrin yayi murabus, daga kan kujerarsa

Sanata  Wabara ya sanar da murabus din ne a yayin fara  taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasa da aka yi yau a Abuja.

Ya ce murabus din da sanata Walid  jibril  yayi, yana bisa doron muradin jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar domin  ganin ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

A yanzu haka, jam'iyyar ta nada tsohon shugaban majalisar dattawa,  Sanata Adolphus Wabara, a matsayin shugaban riko na kwamitin amintattu na jam’iyyar  PDP, da aka fi sani da BOT.

Murabus din Jibril ya zo ne a daidai lokacin da jiga-jigan jam’iyyar PDP na kudancin kasar  nan suke ta neman shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu ya sauka daga kan kujerar shugabancin jam’iyyar domin dora  dan kudancin kasar nan.

 

Gwamna Wike na Jihar Ribas.

To sai dai kuma, kwamitin Kolin jam’iyyar PDP na kasa ya kada kuri’ar tabbatar da nuna goyon baya ga shugabancin Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar,  Inda  ya baiyana cewa ko kusa shugaban ba zai sauka daga kan kujerarsa a yanzu ba.

Shugaban marassa rinjaya a zauren majalisar Wakilai Ndudi Elumelu ne ya gabatar da kudirin kada kuri’ar a yayin taron kwamitin da aka yau a Abuja.

Kudirin ya samu goyon bayan wakilin kwamitin daga jihar kwara wanda mukaddashin shugaban riko na kwamitin Adolphus Wabara ya jagoranta.

Akwai dai tarin kiraye-kiraye musamman daga dattawan jam’iyyar da suka fito daga  kudancin kasar nan, akan shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya sauka daga kan mukaminsa.

 

More from Labarai