On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamna Samuel Ortom Ya Zargi Atiku Abubakar Da Yi Masa 'karya

GWAMNA SAMUEL ORTOM DA ATIKU

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya nemi afuwar sa bisa zargin sa da yi masa karya.

Gwamna Ortom ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata kungiyar matasan Jemgbagh, a yayin  wata zanga-zangar da suka gudanar zuwa  gidan gwamnatin jihar dake  Makurdi, kan karyar da suka ce Atiku ya yi masa.

Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasar ya  fito filo  ya nemi afuwar gwamnan  kan zargin da ya yi na cewa ‘yan uwansa na satar shanun makiyaya a jihar.

Ya soki  ikirarin da  Atiku ya yi na cewar, Gwamnan yayi All..h wadai da daukacin Fulani , yana mai cewa bai taba fadin haka ba.

Sai dai kuma  Gwamna Ortom ya ce duk da rikicin da PDP ke fama da shi, zai yi kokarin ganin ta samu nasara a dukkan matakai a jihar.