On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamna Sanwo-Olu Ya Amince Da Karin Kashi 20 Na Albashi Ga Ma'aikatan Jihar Legas

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya amince da aiwatar da karin kashi 20 na albashin ma’aikatan jihar.

Ma’aikatan sun hada da na ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi da kuma hukumar kula da ilimin bai daya ta SUBEB.

Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2023.

Shugaban ma’aikata na jihar, Hakeem Muri-Okunola, a wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 202 ga watan Maris na 2023, ya ayyana shirin aiwatar da karin albashin.

Haka kuma, za a biya basussukan watan Janairun 2023 tare da Albashin watan Maris,  yayin da kuma na watan Fabrairu,  za a biya tare da albashin watan Afrilu