On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamna Sanwo-Olu Zai Karawa Ma'aikatan Jihar Legas Albashi

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da shirin karin albashi ga  ma’aikatan gwamnati a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya a yayin da ya ke rangadi a sakatariyar Alausa domin tattaunawa da ma’aikatan gwamnati a da nufin inganta ‘Da’a da nagartar aiki da kuma ganin yanayin da suke ciki.

A cewar gwamnan, shirin kara albashin ya biyo bayan tabarbarewar tattalin arzikin da Najeriya ke fama da shi wanda ya sa rayuwa ke wahala ga ‘yan kasa.

Wakilinmu na gidan gwamnatin jihar ya ruwaito cewa, a yayin da yake amsa bukatun da shugaban ma’aikatan Mista Hakeem Muri-Okunola ya gabatar, gwamnan ya kuma bayar da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za’a fitar da motocin ma’aikata ga Daraktoci, moriyar da aka hanasu alfana  kusan shekara bakwai baya.