On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamna Wike Ya Ce Har Yanzu Bashi Da 'Dan Takarar Shugaban Kasa

GWAMNA WIKE

Ana cikin zaman fargaba a jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas, kan dan takarar shugaban kasa da gwamnan jihar Nyesom wike, zai nuna goyon bayansa akai yayin zabe mai zuwa.

A jiya ne gwamnan ya bukaci daukacin magoya bayan jam’iyyar PDP dake jihar dasu tabbatar sun zabi dan takarar gwamna da  ‘yan majalisar  wakilai na jam’iyyar  PDP da suka fito daga jihar.

To sai dai kuma ya bukaci dasu dan tsahirta masa, domin jin  wanda zasu goyi baya a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Da yake jawabi a yayin bude wata  hanya  wadda  ta tashi daga  Ogbodo zuwa Igwuruta , gwamna Wike ya  ce  har  yanzu yana kan  tattaunawa game da wanda zai zaba a matsayin shugaban kasa.