On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamna Wike Ya Nada Mutane Dubu 14 A Matsayin Masu Bashi Shawara

Gwamna Wike

Wata sanarwa da Mataimaki na musamman na musamman ga gwamnan kan harkokin yada Labarai, Kelvin Ebiri, ya fitar, Yace sabbin masu bayar da shawarar zasu taka rawar gani a gwamnatin.

Sanarwar ta kara da cewa baya ga nadin sabbin masu bada shawara dubu 14 da gwamna Wike yayi, Kazalika ya amince da nadin  mutane  dari ukku da goma sha tara, a matsayin masu kula da ofisoshin gwamnati dake mazabun jihar, inda sanarwar ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.

Idan ba’a manta ba a cikin watan  Maris din bana ne, Gwamna Wike  ya baiyana cewa  gwamnati zata bawa mutanen dake son yin aiki tare dashi mukamai, la’akari da cewar ya cika dukkanin alkawuran da  ya daukarwa jihar.