On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnan Babban Bankin kasa Ya Roki Kungiyar Kwadago Ta Janye Shirinta Na Yin Zanga-Zanga Kan Karancin Takardun Kudi

EMEFIELE

Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, ya roki ministan kwadago, Chris Ngige, da ya temaka ya dakile yunkurin shugabancin kungiyar kwadago ta kasa NLC kan zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranar Laraba.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Juma’ar da ta gabata ne, shugabannin kungiyar ta NLC suka baiyana cewar  zasu rufe daukacin  rassan bankin a fadin kasar saboda karancin kudi da ake fama da shi a Najeriya.

Sai dai a wata ganawar sirri  da aka yi a ma’aikatar kwadago da ke Abuja a ranar Litinin, Emefiele ya ce zanga-zangar za ta kawo cikas ga ci gaban babban bankin idan ba a dakile tab a.

A  yayin ganawar akwai  Shugaban  kungiyar  kwadago Joe Ajaero yayin da Emefiele ya jagoranci jami’an babban bankin zuwa taron wanda Ministan ya jagoranci  ganawar.

Har zuwa wannan lokaci  babu wata sanarwa a hukumance da aka fitar  kan ko an cimma wata matsaya ko kuma akasin haka.