On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnan Jihar Kogi Ya Bada Umarnin Rufe Gidajen Masu Yawon Ta-Zubar A Fadin Jihar

GWAMNAN KOGI YAHYA BELLO

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello Ya bada umarnin rufe daukacin Gidajen masu yawon Ta zubar dake fadin jihar.

Kazalika ya haramta  saka Takunkumi a wuraren taruwar jama’ar  domin tabbatar da ana gane kowa a jihar. Daukar matakin ya biyo barazanar rashin tsaro  da jihar take fuskanta a yan kwanakin nan.

Gwamnan ya bada wannan umarni ne a ranar Talata a birnin Lokoja yayin wani taro da aka shirya kan harkokin tsaro, tare da daukacin  masu rike da sarautun gargajiya da kuma shugabannin kananan hukumomi na jihar.

Gwamna Bello  ya bada umarnin rushe daukacin  wuraren  ‘yan kama wuri zauna dake sana’ar yawon Ta zubar a Lokoja da Osara sai Zango da Itobe da Obajana da kuma dukkanin inda suke a jihar.

  

More from Labarai