On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnati Da Bankin CBN Basu Da Wata Matsaya Sai Bayan Hukuncin Kotun Koli Kan Chanjin Kudi - Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban kasa tace gwamnatin tarayya za ta bayyana matsayarta akan tsarin chanjin kudi na Naira bayan yanke hukunci a Kotun Koli yau laraba.

Mai magana da yawun shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, yace gwamnatin tarayya ko kuma babban bankin kasa CBN ba su da wata matsaya kan cigaba da yin amfani da tsaffin takardun kudi na Naira saboda shari’ar da ake yi.

Wannan dai na zuwa ne kimanin mako guda bayan da kotun kolin  ta bada umarnin a ranar 8 ga watan Fabrairu, inda ta dakatar da wa'adin da babban bankin CBN na ranar 10 ga watan Fabrairu na dakatar da amfani da tsofaffin takardun kudi na naira.

‘Yan Najeriya za su san makomarsu kan takardun na Naira nan gaba a yau Laraba.

A zamanta na Yau Laraba Kotun Kolin ta shigar da karin  jihohi tara a matsayin masu shigar da kara  akan Karar da gwamnatocin Kaduna da  Kogi da kuma Zamfara ke kalubalantar wa'adin chanjin takardun kudi na Naira.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Nasir El-Rufai da Yahaya Bello na Kaduna da Kogi suka halarci zaman kotun Kolin a yau.

Mai shari’a John Okoro dake jagorantar Alkalai  tara,ya amince da shigar da manyan lauyoyin jihohin Katsina Legas da Ondo da Ogun da Ekiti da kuma Sokoto a matsayin masu shigar da kara.

Kotun ta umarci masu gabatar da kara na asali da wanda ake kara da sukakunshi Babban Lauyan Tarayya da su gyara sauran Karar ta farko domin sanya  sabbin bangarorin.