On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnati ta san abun da muke bukata - maharan jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna

Ta cikin wani Video na kasa da minti 2 da suka fitar da Maraicen ranar laraba

 

‘Yan ta’adda da sukayi awon gaba da Fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a karshen watan da ya gabata, sunyi barazanar hallaka mutanen da sukayi garkuwa da su muddin gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatunsu

Ta cikin wani Video na kasa da minti 2 da suka fitar da Maraicen ranar laraba, ‘yan bindigar sanye da kakin Sojoji sunce ba kudi ne a gabansu ba kuma gwamnatin tarayya na da masaniya akan abunda suke bukata.

Mutane 4 aka nuna daga cikin ‘yan bindigar a ciki Vidiyon tare da Fasinja guda 1 da suka Sace Alwal Hassan shugaban  bankin Manoma na kasa,  sunce sun saki Alwal Hassan saboda yawan shekarunsa da kuma alfarmar watan Ramadan.

Da alama an dauki Vidiyon a wata cibiyar dakarun sojoji ta Birnin Gwari dake Kaduna wadda aka kaiwa hari a ranar Litinin, inda ake iya hango daya daga cikin tankar yaki ta sojoji da aka lalata yayin harin..
Da yake magana bisa umarnin ‘yan ta’addan, Alhaji Alwal Hassan yace sun sakeshi ne soboda tausayawa.