On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Jihar Anambra Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Zargin 'Daliba Da Karawa Kanta Makin Jarabawar UTME

Gwamnatin Jihar Anambra ta kafa wani kwamitin bincike kan cece-kucen da ya biyo bayan zargin kara maki da ake yiwa wadda tafi kowa hazaka a jarrabawar UTME ta shekarar 2023.

A baya an sanar da cewa Ejikeme ‘yar shekara 16 daliba a makarantar sakandaren ‘yan mata ta Anglican da ke Nnewi ta samu maki 362 a matsayin wacce ta fi kowacce kokari.

Sai dai a wata sanarwa da hukumar JAMB ta fitar, ta yi watsi da sakamakon nata a matsayin na bogi, inda ta ce an yi magudi kuma za a gurfanar da ita a gaban kuliya.

Sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Anambra ta fitar dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a Mr Nnaemeka Egwuonwu, ta bayyana cewa binciken zai bankado gaskiyar yadda Ejikeme ta samu sakamakon nata.