On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Jihar Kano Ta Gargadi Ma'ikatan Kananan Hukumomi Kan Rashin Zuwa Aiki

Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi ga ma'aikatan kananan hukumomi kan rashin zuwa aiki.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya yi gargadin  lokacin da yake kaddamar da taron bita na kwanaki hudu ga muhimman  jami’an kananan hukumomin jihar Kano a Kaduna ranar asabar.

Ya bukaci kananan hukumomi su kara kaimi wajen samar da kudaden shiga na cikin gida domin hanzarta wanzar da cigaba a sassa daban-daban na  jihar.

A wata sanarwar  manema labarai mai dauke da sa hannun babban jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar kananan hukumomi da sarautun gargajiya, Dahiru Lawal Kofar Wambai ya fitar, mataimakin gwamnan ya yi gargadin cewa za a kai ziyarar bazata a ofisoshin manyan jami’an  domin dakile rashin zuwa aiki.

A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da sarautun gargajiya a jihar Kano, Yusuf Datti Hussain ya bukaci ma’aikatan su yi amfani da abin da dabarun da suka koya wajen gudanar da ayyukan da aka dora musu.

A wani bangaren kuwa, masu ruwa da tsaki na bada shawarar raba hanyoyin tattara kudaden shiga na jiha da kananan hukumomi da samar da rumbun bayanai a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Shawarar ta fito ne ta cikin sanarwar bayana taro da shugaban kwamitin, shugaban karamar hukumar Bichi, Farfesa Muhammad Sabo ya gabatar a wajen rufe taron bita na yini biyu da aka shirya wa manyan ma’aikatan kananan hukumomi na jihar Kano a kaduna.

Sun ba da shawarar samar da tsarin sa ido na ciki da waje domin kawar da rashin dorewa da cin hanci da rashawa a bangaren tara kudin shigar.

Da yake nasa jawabin daraktan horas da ma’aikata, Isa Musa Kera, ya bada tabbacin nuna kulawa ta musamman kan bada horo domin  amfanin al'ummar jihar baki daya.