On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Jihar  Kano ta Koka akan Yawaitar Karkatar da gidajen Sauro Zuwa Amfani Da su Wajen Kare tsirrai Yayinda zazzabin Cizon Sauro Ya yi Ajalin Mutane 631 a Jihar

Ya ce sama da masu ziyartar  asibiti miliyan 2.8 a cikin 2021 rashin lafiyarsu nada  alaka da cutar. 

 

Yaki da cutar zazzabin cizon sauro mai saurin kisa na iya ci gaba da rashin Tasiri ko  haifar da  sakamako da bai taka Kara ya karya ba a jihar Kano saboda abin da gwamnatin jihar ta bayyana a matsayin kafiya wajen sauya halayen wasu al'ummar jihar.

Da yake zantawa da manema Labarai a wanj bangare na Ranar yaki da Zazzabin cizon Sauro a bana, Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa,  ya ce a shekarar 2021 kadai mutane 631 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a jihar. 

Ya kara da cewa an sake samun wasu mace-mace 96 a cikin zango farko na shekarar 2022.

Yace  "A cikin shekarar 2021, Mutanen da suka kamu da cuta mai alaka da zazzabin cizon sauro sun kai milliyan 2 da dubu 836 da 761 daga cikinsu, milliyan 2 da dubu 66 da 357 daidai da kashi (97.5%) sun kamu da cutar zazzabin cizon sauro, kuma an yi musu magani da ACT inda aka samu  mutuwar mutane 631, yayinda aka samu Mutane 96 na mace-mace a Zango farko na shekarar  2022". 

Masu cutar zazzabin cizon sauro miliyan 2.8 sun ziyarci asibitocin Kano a shekarar 2021 kadai.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a da Kula da Cututtuka, Dakta Hashiru Rajab, ya danganta kusan kashi 60% marasa lafiya  a Kano da cewa sun kamu da cutar zazzabin cizon sauro. 

Ya ce sama da masu ziyartar  asibiti miliyan 2.8 a cikin 2021 rashin lafiyarsu nada  alaka da cutar. 

Ya bayyana kokarin gwamnatin jihar na dakile yaduwar cutar wanda suka hada da bayarda magungunan rigakafin cutar zazzabin cizon sauro milliyan  13 da dubu 110 da 365 kyauta ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar da kuma shirye-shiryen da ake yi na raba wani rukunin gidajen Sauro masu dauke da magani sama da miliyan takwas kyauta  ga mazauna jihar.

Sai dai ya bayyana damuwa da cewa Jama'a Suna sayar da gidan Sauro da aka basu kyauta a farshin Naira 200  wanda aka samar kan Naira dubu 5.

Da aka tambaye shi ko me yasa yaki da zazzabin cizon sauro ba ya tasiri ko ke haifar da sakamakon da bai taka kara  ya karya ba a jihar Kano  duk da makudan kudade da ake kashewa wajen gangamin yaki da cutar a kowacce shekara, kwamishinan ya dora laifin rashin nuna kishi da kulawa tsakanin mazauna jihar  kan tallafin da ake samarwa.

Dokta Tsanyawa ya shaida wa Arewa Radio cewa duk da raba gidajen sauro miliyan takwas mai dauke da  magani  kyauta a kowacce shekara hudu, binciken ya nuna cewa mazauna jihar  da dama na karkatar da amfanin Gidan Sauron zuwa wasu Abubuwa na daban. 

A cewarsa, wasu manoma daga cikin wadanda suka amfana suna amfani da gidajen sauron wajen kare shukar su, wasu mata na mayar da shi labule, yayin da wasu ke siyar da gidajen sauron na  kimanin Naira dubu  5 akan kudi Naira 200.

Haka kuma ya shawarci iyaye da su fito da  ‘ya’yansu masu shekaru 3 zuwa 9 a zagayen  kwanaki 4 da za'a gudanar  na rarraba magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro, wanda ke fatan cimma yara milliyan 3 da dubu  193 da 2 daga watan Yuli zuwa Oktoba na shekarar 2022.

More from Labarai