On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Jihar Kano Ta Rabawa Asibitocinta Kayan Kiwon Lafiya Na Naira Milyan 15

DR. Aminu Ibrahim Tsanyawa Kwamishinan Lafiya Na Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta rabawa asibitocin jihar Kano da kayayyakin kiwon lafiya kyuata na kimanin Naira miliyan goma sha biyar.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Asibitoci ta jihar Kano Dr Nasiru Alhasan Kabo shine  ya bayyana haka a lokacin da ya kaddamar da rabon kayayyakin ga asibitocin a nan  Kano.

Kabo wanda Daraktan kula da  sashin Likitanci na hukuamr, Dr Sulaiman Mudi Hamza ya wakilta ya ce za a yi amfani da kayayyakin ne a wuraren kula da mata masu juna biyu, da sashin bada agajin gaggawa  na asibitoci da kuma kula da lafiyar kananan  yara. 

Wakilinmu  Bashir Faruk Durumin Iya ya ruwaito mana  cewa wata kungiya mai zaman kanta dake karkashin Asusun amintattu na  kula da bangaren Lafiya ta ba da gudummawar Naira Milyan 5m domin aiwatar da  shirin.

More from Labarai