On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Jihar Kano Ta Rufe Babban Kantin Sayar Da Kayayyaki Saboda Kin Karbar Tsohon Kudi

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani babban katin sayar da kayyaki saboda kin amincewa da karbar tsofaffin takardun kudi na  naira

Gwamnan ya bayar da umarnin rufe babban kantin na Wellcare saboda kin karbar tsoffin takardun naira daga masu zuwa siyayya.

Shugaban hukumar kare hakkin masu sayen kayayyaki a Jihar Kano, Baffa Babba ‘Dan-Agudi, ya shaidawa manema labarai bayan rufe wurin cewa za a dauki matakin shari’a akan babban kantin.

‘Dan Agudi ya gargadi sauran ‘yan kasuwa a Kano cewa gwamnatin  ba ta hana amfani da tsohon kudi na naira  ba, saboda haka duk wani shago da aka kama yana kin karbar tsohon kudi na  naira za’a dauki mataki akansa.

Da suke mayar da martani, mahukuntan babban kanti sun bada hakuri, inda suka roki gwamnan Ganduje da ya sake bude wurin  kasuwancin yayinda sukayi alkawarin yin abin da ake bukata.