On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Jihar Kano Zata Fasalta Shirin Inshorar Lafiya Ga Marasa Karfi BHCF

Gwamnatin jihar Kano za ta sake fasalta yadda ake aiwatar da shirin Asusun Kula da Kiwon Lafiya ga marasa karfi  na BHCF don magance gibin da aka gano.

Sakatariyar zartarwa ta hukumar taimakekeniyar lafiya a jihar Kano KSCHMA Dr. Rahila Muktar, itace ta sanar da hakan a wajen bude horon kwana 3 kan hanyoyin samar da kudaden tafiyar da harkokin kiwon lafiya da inshorar lafiya wanda hukumar ta shirya tare da tallafin cibiyar CHESDA domin gina kwazon  ma'aikata.

Dokta Rahila Muktar wadda Darakta a hukumar Dr. Fatima Zaharadden ta wakilta, tace sake bibiyar shirin zai kunshi tantance masu cin gajiya tsarin da kuma yin gyare-gyare ta yadda za’a cimma ka'idoji da tsare-tsaren kasa.

Ta kara da cewa gwamnatin jihar Kano ta yi tanadin karfafa hukumar da kuma shirin, inda ta bukaci kungiyoyin kwadago na jami’ar Yusuf Maitama Sule da bangaren shari’a da  Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil da su bada hadin kai ga Hukumar KSCHMA domin morewa Kula da Lafiya cikin sauki ga mambobinsu.

Da yake jawabi tun da farko Jami’in hukumar inshorar lafiya ta kasa Alhaji Ibrahim Aliyu Alhassan ya yabawa KSCHMA bisa shirya horon.