On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Jihar Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Kisan Wani Dagaci

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya ayyana dokar hana fita daga garin Lambata da ke karamar hukumar Gurara bayan wani kazamin rikici da ya kai ga kashe wani Dagacin kauyen Mohammed Abdulsafur.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Ahmed Matane ya fitar ranar Lahadi a Minna babban birnin jihar.

Rahotanni sunce  wasu ‘yan bata gari sun kashe dagacin  kauyen Lambata a ranar Asabar a yayin wani rikici da ya barke.

Bello ya bayar da umarnin a sanya dokar hana fita a garin daga karfe 6 na yamma  zuwa 6 na safe, daga ranar Lahadi, har zuwa abunda hali ya yi.