On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Bada Hutun Mako ‘Daya Domin Yin Rijistar Katin Zabe

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bai wa ma'aikatan jihar hutun mako ɗaya domin su yi rajistar katin zaɓe da ake gudanarwa yanzu haka a sassan faɗin Najeriya.

 

Bayanin matakin na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Kwamashinan Yaɗa Labarai na Jihar Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar ranar Asabar a Gusau.

Ya ce Gwamna Bello Matawalle ya amince da ba da hutun ne daga Litinin, 20 zuwa 24 ga watan Yuni.

A Sakamakon wannan sanarwa, an umarci dukkannin kwamashinoni da masu bai wa gwamna shawara da sakatarori da sauran ma'aikatan gwamnati da jami'an jam'iyyun siyasa da su saka ido kan yadda aikin rajistar ke gudana.

Ƙungiyoyi da 'yan gwagwarmaya na ci gaba da yin kira ga hukumar zaɓe ta ƙasa INEC  ta tsawaita wa'adin yin rajistar, suna masu cewa mutane da dama ba su samu damar yi ba saboda ƙarancin kayan aiki da kuma cunkoso.

INEC ta saka ranar 30 ga watan Yuni da mu ke ciki a matsayin ranar ƙarshe da za a rufe aikin rajistar.