On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Kano Ta Bada Hutun Sallah Na Kwana 10 Ga ‘Daliban Makaranta

Gwamnatin jihar Kano ta amince hutun kwana 10 ga daukacin makarantun gwamnati na firamare da sakandire da masu zaman kansu domin shagulgulan babbar Sallah..

 

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano itace ta tabbatar da amincewar  ta cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai Aliyu Yusif ya fitar, an sanar da Iyaye da masu kula da yara da ‘Daliban makarantu cewa hutun zai fara ne daga ranar Alhamis 7 zuwa Lahadi 17 ga watan Yuli na shekarar  2022.

Ma’aikatar ta umurci duk daliban SS3 da ke rubuta jarabawar NECO da NABTEB da NBAIS da kuma daliban da ke makarantun hadaka aka dawo su makarantun GSS Gwarzo da GGSS Shekara su ci gaba da zama a makarantunsu.

Hakazalika ma’aikatar ta umurci dukkan shugabannin makarantun kwana da su tabbatar da cewa daliban kwana sun koma makarantunsu a ranar Lahadi 17 ga wata sai ‘yan jeka ka dawo  a ranar Litinin 18 ga watan Yuli na 2022, domin cigaba da harkokin koyo da koyarwa ba tare da wani bata lokaci ba.

Sai dai kuma ma’aikatar ta yi gargadin cewa za a dauki matakin ladabtarwa a kan daliban da suka gaza komawa makaranta a ranar da hutun ya kare.