On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Kwararru Kan Lalacewar Tituna

Gwamnatin jihar Kano tace za ta kashe sama da Naira biliyan 1 da milliyan dari 2 wajen gyara shatale-tale da kuma wasu manyan tituna da ke cikin mummunan yanayi a kwaryar birni.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa a yau, yace shatale-talen  sun hada da na kuaa da gidan mai na A A Rano a karshen titin Audu Bako  sai Wanda ke  kusa sa  First Bank daura da bank Road da dai sauransu.

Sauran  hanyoyin sun hada da Audu Bako Way da  Sani Marshal Road da  Mission Road da  Hotoro Tsamiyar Boka da  Layin Kaura Goje da Sheikh Hassan-Layin Gidan Biredi zuwa titin Sani Bello da Kwanar Jaba zuwa Kwana Hudu zuwa Gayawa gada  da dai sauransu.

Garba ya ce hakan ya biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya haifar da ambaliya a fadin jiha Kano

A cewarsa, an kafa wani kwamitin kwararru da ya kunshi injiniyoyi daga ma’aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa da  hukumar tsara birane ta jiha da kuma wasu ma’aikatu da  sassan da hukumomi domin nazarin halin da ake ciki da nufin daukar matakin gaggawa.