On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Kano Za ta Aiwatar da Hukuncin Kisa akan Wanda ake Zargi da Kone Masallata da Zarar Kotu ta Kama Shi da Laifi

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin rattaba hannu akan hukuncin kisa ga mutuminan da ake zargi da bankawa masallata guda 23 wuta a wani masallaci dake garin Larabar Abasawa da zarar kotu ta same shi da aikata laifin.

Gwamna Yusuf, wanda ya bayyana kone masallatan a matsayin rashin Imani marar musaltuwa, ya bawa jami’an tsaro shawara akan su gurfanar da shi a kotun shari’ar musulunci domin ya girbi abin da ya shuka.

“Duk abunda doka tace ayi akan wanda ya kashe al’uma, sai mun tabbatar da shi akan sa. Kuma ina so jami’an tsaro su kaishi kotun addinin musulunci, a gabatar da shi, a tabbatar an yi masa shari’a gwargwadon abunda doka ta shari’ar musulunci ta ce a yiwa wanda ya yi kisa. Mu kuma ba za mu jinkirta ba, duk abunda kotu ta yanke, za mu rattaba hannu akai.”

Arewa Radio ta rawaito cewa, saukar gwamnan daga birnin tarayyar Abuja ke da wuya, bai tsaya a ko ina ba, sai asibitin Murtala Mohammad dake kwaryar birnin Kano domin jajantawa wadanda wannan ibtila’I ya rutsa da su.

Yayin da yake rarraba tallafin kudi na naira dubu 100 ga marasa lafiyan domin siyan ‘yan ababan da suke bukata, gwamnan ya yi karin hasken cewa al’amarin ba shi da nasaba da siyasa ko wani nau’I na ta’addanci, yana mai jaddada cewa rikicin gado ne ya kai ga cinna wa masallatan wuta.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mutane 15 daga cikin 23 da suka kone sakamakon kunar da suka sha sun mutu, yayinda mutane 8 ke cigaba da karbar magani a asibitin Murtala dake nan Kano.

Gwamnan ya lashi takobin tallafawa marasa lafiyan har Allah ya tashi kafadun su tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kaucewa afkuwar hakan a nan gaba.