On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Kano Za ta Kammala Aikin Gyaran Makarantu 120 Kafin Komawar Dalibai Makaranta

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Lokacin da ya kai ziyarar duba aiyuka

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin kammala aikin gyaran ajujuwan karatun dalibai da ta ke gudanarwa yanzu haka a makarantu guda 120 kafin a koma makarantu domin cigaba da zangon karatu na gaba.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a ranar Talata, lokacin da ya kai wata ziyarar ba zata wasu makarantu da ake gudanar da wadannan aiyuka.

Manufar ziyarar, a cewar kwamishinan, ita ce dubawa tare da tantance nagartar aiyukan da ake gudanarwa da kuma tabbattar da cewa ‘yan kwangilan za su iya kammala aikin a lokacin da aka ware wa aikin, kafin dalibai su koma makarantun su.

Yayinda yake yabawa da yadda aikin ke gudana jim kadan bayan kammala zagayen, Doguwa ya ce gyaran makarantun wani bangare ne na cika alkawarin da gwamnan ya daukar wa al’umar jihar Kano na farfado da martabar ilimi a jihar Kano.

Sai dai ya bukaci da a gudanar da aiki na musamman a makarantar masu bukata ta musamman ta Tudun Maliki, wanda zai saukakawa daliban zirga-zirga da kuma koyon karatu.

Ya kuma kara da cewa wannan ba ita ce ziyarar farko da muka kai domin duba yadda wadannan aiyuka ke gudana ba, yana mai karawa da cewa suna yin hakan ne domin yin nazari akan gyarae-gyaren da ake gudanarwa.

Kwamishinan ya ce yayin wannan ziyara, an sa yan kwangila su gyara wasu abubuwa da aka gano cewa ba zasu yi karko ba, tare da kara kudade a wuraren da ake da bukata, gudun kada a yi aikin baban giwa.

COMMISSIONER EDUCATION 3

”Ga duk wanda ya ga yadda ake wannan aiki, zai ga cewa aiki ne ake yi mai nagarta kuma ba almundahana a ciki, kuma na ba da dadewa za mu kammala wadannan aiyuka baki daya”.

Kwamishina Doguwa, ya kuma kara da cewa “ya zuwa wannan lokaci, an kammala wasu daga aiyukan kuma ana dap da karasa sauran da ake yi yanzu, sannan bayan nan za’a fara sabbin aiyuka da za su samar da kyakyawan muhallin karatu ga dalibai.”

Makarantun da kwamishinan ya ziyarta sun hadar da makarantar Primare da karamar Sakandire dake unguwar Gandun Albasa, Makarantar kurame dake Tudun Maliki, Governor’s College a unguwar Kofar Nasarawa, First Lady’s College da kuma Makarantar Sakandiren ‘yan mata dake Jogana.

Aiyukan da ake gudanarwa a makarantun sun hadar da ginin katangu domin ba su kariya, gyaran ajujuwa da rukunin ajujuwa da suka lalace tsahon shekaru, ginin dakunan taro a wasu, samar da kujeru da teburan zama da kuma gyaran dakunan gwaje-gwaje.

Haka nan, kwamishinan ya tsaya a makarantar nan da ake kula da kuma koyar da yara daga Arewa maso gabas, wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su, domin duba lafiyar su da kuma alkawarin cigaba da basu kulawar da ta kamata.

COMMISSIONER EDUCATION 2