On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Kano Zata Rabawa Mata Awaki Domin Dogaro Da Kai

AWAKI

Gwamnatin jihar kano ta amince da biyan naira milyan 700 a matsayin kudin makaranta ga Dalibai yan asalin jihar Kano dubu bakwai dake karatu a jami’ar Bayero ta nan Kano.

A wani sako da  ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter,  Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Ya ce matakin wani bangare ne na  saukakawa al’umma kan halin tsadar rayuwa da ake ciki.

Ya  kara da cewar za’a tsara yadda matakan  tsarin bada tallafin karatun zai kasance a nan gaba kadan.

A wani bangaren kuma, Gwamnatin jihar kano na wani shiri  na samar da shanu da  Tumaki da kuma  Awaki domin baiwa  mata  musamman a yankunan karkara,da zummar  ganin sun dogara da kansu  da kuma samun cigaban tattalin arziki.

Wannan dai wani bangare ne  na rage  radadin janye tallafin man fetir da aka yi, kamar  yadda  gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf ya  baiyana,  a yayin zaman majalisar zartawa  na  wannan makon da aka yi jiya a gidan  gwamnatin kano.

Ya kuma  ce   gwamnatin jihar Kano  ta sayi  hatsi  na kimanin naira bilyan 1 da milyan 600 ,wanda  ya hada da Gero  da  Masara da  Shinkafa domin raba su kyauta  ga al’ummar  kano.

A wata sanarwa da kakakin  gwamnan kano,Sanusi Bature  ya fitar,  Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin taraiyya da  ta sake  yin nazari  kan  yadda  ta yi  tsarin rabon tallafin rage  radadi a tsakanin jihohin kasar nan.

Sai dai ya godewa  gwamnatin  shugaban kasa  Bola Tinubu  kan tallafin da  ta samar,  tare da bada shawarar a  baiwa jihar kano kaso mai tsoka  kasancewar  yawan jama’ar  da   take  das u.