On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Legas Zata Kashe Milyan 61 Domin Binnen Mutanen Da Suka Mutu A Zanga-zangar END SARS

SARS

Yanzu haka jama’a na cigaba da yama’di-‘di da matakin da gwamnatin jihar Legas ta dauka na amincewa da kashe zunzurutun kudi har naira naira milyan 61 da dubu 200, domin yin gagarumin bukin binne mutane 103, wadanda suka gamu da ajalinsu a shekarar 2020, sakamakon zanga-zangar ENDSARS, data barke a jihar.

Idan ba’a manta ba, Gwamnatin jihar da kuma rundunar soji ta kasa sun ga baiken rahoton da kwamitin bincike   ya fitar, wanda ya nuna  cewar  anyi kisan kiyashi a yankin Lekki Toll Gate, a lokacin da sojoji  suka bude  wuta, a ranar 20 ga watan Octoban  2020.

Sai dai wata wasika da mai dauke da kwananan wata,19 ga watan da muke ciki,da hukumar kula da bada kwangilolin gwamnati ta jihar Legas ta fitar, Ta nuna cewar,gwamnatin jihar  ta dauki hayar wani kamfani mai suna Tos Funeral Ltd, domin yin aikin binne  mamatan guda  103 akan kudi naira milyan 61 da dubu  200.

Wasikar dai ta haifar da cece kuce a tsakanin mutane, musamman masu  ‘yan gwagwarma ya, wanda  ke nuna rashin amincewarsu da daukar matakin, duk da cewar  a baya gwamnati da hukumomi sun musanta cewar anyi kisan kiyashi a wajen.

A wani bangaren kuma, Gwamnatin jihar Legas  ta mayar da martani kan cece-kucen da jama’a  ke  yi dangane da fitar da makudan kudin domin binne gawarwakin mutanen.

Wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar Lafiya ta jihar Legas, Dr Olusegun Ogboye ya fitar a daren jiya,  Ta yi ikirarin cewar   daga cikin mutanen  103 da suka mutu, babu wanda aka samu a yankin Lekki Toll Gate.

Bugu da kari yace gwamnatin jihar  ta amince  da shirya  yin  gagarumin bukin binne mutanen ne a  lokaci daya, bayan kwashe  shekara  ukku  ana gaiyatar  yan uwa da masoyan  wadanda  ba’a gani ba a lokacin zanga-zangar, amma kuma babu wanda  ya je  domin duba  dan uwansa  ko wani nasa  da  ba’a gani ba saboda zanga-zangar.