On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Najeriya Ta Bukaci Kungiyar Kwadago NLC Ta Daina Adawa Da Sabbin Kungiyoyi 2 Da Aka Yiwa Rijista A Tsarin Jami'oin Kasar

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyar kwadago ta kasa NLC da ta janye adawar da ta ke yiwa sabbin kungiyoyin malaman Jami’oi guda biyu CONUA da NAMDA da aka yiwa rajista a tsarin jami’o’in gwamnati a Najeriya.

Ministan Kwadago Sanata Chris Ngige, shine ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jam’a na ma’aikatar kwadago, Mista Olajide Oshundun,  ranar Talata a Abuja.

Sai dai a wata wasika da shugaban NLC, Ayuba Wabba ya aikewa Ngige, ya bukaci a janye rijistar da aka yiwa sabbin kungiyoyin, bisa hujjar cewa rajistar su ta saba wa dokokin dake jagorantar kungiyar kwadago.

A martaninsa, a ranar 12 ga Octoba, Ngige ya roki NLC da ta bar sabbin kungiyoyin su wanzu cikin ‘Yanci kamar kowacce kungiya.

Ministan ya dage kan cewa dokar warware rigingimun kwadago ta shekarar 2004 ta ba shi ikon yin rajistar sabbin kungiyoyin kwadago, ko dai ta hanyar yi wa sabuwar kungiya rijista ko kuma sake fasalin  wadanda ake da su.