On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Najeriya Ta Fusata Kungiyar ASUU

Kungiyar malaman jami’o’i ASUU da kwamitin  shugabannin jami’o’in Najeriya sun yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na cire kashi 40 daga kudaden shiga na jami’o’i.

Gwamnatin tarayya, a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 17 ga Oktoba, 2023 mai dauke da sa hannun Akanta-Janar ta Tarayya, Mrs Oluwatoyin Madein, ta ce za ta fara cire kudin daga watan Nuwamba na  2023 kamar yadda daftarin kudi na ranar 20 ga watan Disambar 2021 ya nuna.

Da yake mayar da martani, Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce matakin da gwamnatin tarayya ta dauka ya fusata kungiyar saboda jami’o’in ba sa samun kudaden shiga daga wasu kuɗaɗe da ake  dawainiyya ga  dalibai.

A nasa bangaren, babban sakataren kwamitin  shugabannin jami’o’in Najeriya Farfesa Yakubu Ochefu ya ce kudaden da ake cirewa a baya sun kai kashi 25 amma yanzu ya karu zuwa kashi 40.

Ya yi kira ga Akanta Janar da ta fayyace abin da ake nufi da yunkurin, yana mai cewa jami’o’in suna karbar kudin dawainiya ne  kawai daga dalibai ba riba ko kudaden shiga ba.