On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Tsaf Domin Cigaba da Harkokin Sufurin Jiragen Kasa Daga Kaduna Zuwa Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce za’a dawo da cigaba da harkokin sufurin jirgin kasa na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna a watan Nuwamba da muke ciki na 2022.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, shi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a yayin da yake bayani kan ayyuka ma’akatar.

Hakan  na zuwa ne wata daya bayan Gwamnatin Tarayya ta ce an sako ragowar fasinjojin da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jirgin kasan a ranar 5 ga Oktoba, 2022.

Ministan ya ce an tanadi matakan tsaron ba dare ba rana ga sufurin jirgin kasan, wanda wata bakwai ke nan da dakatar da shi.

Ministan ya kara da cewa hukumarsa ta koyi darussa daga harin da aka kai wa jirgin kasa a watan Maris, lamarin da ya sa aka dakatar da sufurin jiragen kasa tsakanin manyan biranen biyu.

Ya ce an tanadi jami'an tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji, to sai dai bai bayyana ainihin ranar da za a fara jigilar ba.

Haka kuma ministan ya ce an yi wani tsari da zai rika lura da zirga-zirgar jiragen kasan da kuma titin jirgin.

Ya kara da cewa, tsarin zai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ma'aikatu da hukumomin gwamnati da jami'an tsaro damar ganin abun da ke wakana a kan titin jirgin ba tare da bata lokaci ba.

More from Labarai