On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Najeriya Tace Ana Samun Cigaba A Tattunawa da Kungiyar ASUU Domin Kawo Karshen Yajin Aiki

Takaddama Kan Yajin Aikin ASUU

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU a kokarinta na ganin an janye yajin aikin da ake ci gaba da yi a jami’o’in Najeriya.

Ministan kwadago Sanata Chris Ngige shine ya bayar da wannan tabbaci a karshen wani taron tattaunawa tsakanin wakilan  gwamnatin tarayya da na kungiyar malaman jami’o’i ASUU da sauran kungiyoyin kwadago na bangaren jami’o’in Najeriya, tare da kungiyoyin masu ruwa da tsaki da kungiyoyin farar hula, kan yajin aikin  da ke ci gaba da gudana a Jami'o'in kasarnan, inda suka tattauna a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja. 

Gwamnatin Tarayya ta yi nasarar jawo hankalin  masu yajin aikin da su amince da yarjejeniyar janyewa yayin da ake kokarin sasanta takaddamar dake tsakanin bangarorin biyu.
 
Koda ya ke shugaban Kungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya ki yin magana da ‘yan jarida kan sakamakon tattaunawar, amma yanayinsa  ya nuna alamar babu wani sabon abu da aka cimma illa iyaka dai  gwamnati tana bukatar ASUU ta janye yajin aikin ba tare da wani bata Lokaci ba, duk da rashin ganin wani abu  a  kasa bukatar da ASUU ta ki amincewa da ita. 

Tun da farko a lokacin da yake jawabi ga shugabannin kungiyoyin da masu ruwa da tsaki a wajen bude taron, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya roki malaman  jami’ar da su janye  yajin aikin tare da amincewa su koma bakin aiki yayin da ake tattaunawa kan bukatunsu. 

Ya ce akwai bukatar a yi wani abu cikin gaggawa domin bude Jami'oi da kuma hana dalibai yin zanga-zanga a kan tituna. 

A cewarsa, barin yajin aikin ya kara daukar Lokaci ba zai zama maslaha ga kowa ba, ya kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci kungiyar ta yi kokarin kawo karshen yajin aikin saboda halin da  makomar dalibai ke ciki.

A nasu bangaren, Shugaban majalissar hadin kan Addinai a kasarnan, Mai Alfarma Sarkin musulmi Alhaji  Sa'ad Abubakar na  IIl da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta kasa CAN Rev Samson Ayokunle sun bukaci ASUU da kungiyoyin ma'aikatan da ba malamai ba su amince da rokon shugaban kasa Buhari tare da dakatar da yajin aikin da suke yi yayin da ake kokarin shawo kan matsalolin da ake takaddama a kai.