On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Najeriya Zata Hana Bankunan Internet Yin Tasarrafi Da Hotuna Da KumaLambobin Wayar Abokan Hulda

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta hana bankunan yanar gizo yin tasarrafi da hotuna da kuma lambobin wayar abokan huldarsu.

Gwamnati ta ce zata umarci Google ya  aiwatar da wannan mataki, ta kara da cewa matakin ya zama wajibi ne don dakile mamaye sirrin abokan hulda da  kamfanonin bada rance na Internet keyi.

Idan za’a iya tunawa a baya-bayan nan hukumar Gasa da kare hakkin masu sayen kayyaki ta kasa ta yiwa shafukan bada Rance 170 Rijista daga cikin 200 da ke aiki a cikin Ć™asarnan.

A cewar Google, daga ranar 31 ga watan Mayu, na 2023, manhajojin lamuni dake akan Play Store za su rasa ikon shiga lambobin masu amfani da su ko hotuna.