On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Najeriya Zata Tattauna Da Gwamnonin Jahohi Kan Yiwuwar Sakin Kashi 30 Na Fursunoni

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, yace zai gana da gwamnonin jihohi domin cimma matsaya kan sakin akalla kashi 30 na fursunonin da ake tsare da su a fadin Najeriya

Aregbesola ya bayyana hakan ne ta cikin wani shirin kamfanin dillancin labaru na kasa a Abuja.

Ministan ya ce, tattaunawa da gwamnonin ta zama dole domin sama da kashi 90 cikin 100 na fursunonin ana tsare da su ne saboda sabawa dokokin jihohi.

Aregbesola ya kuma ce sama da kashi 70 cikin 100 na fursunoni dubu 75 da 635 a halin yanzu suna jiran shari’a.