On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Taliban Na Neman Dauki Sakamakon Girgizar 'Kasa

Taliban

Gwamnatin Taliban dake kasar Afganistan ta bukaci samun tallafin kasashen duniya, a daidai lokacin da kasar ke tunkarar ibtila’in girgizar kasa wanda ya kai karfin maki 6.1.

Fiye da mutane 1,000 suka mutu sannan kuma  Dubu 1 da 500 suka jikkata, a yayin da  baraguzan gidaje  suka binne wasu.

Lardin Paktika da ke kudu maso gabashin kasar ya fi fama da ibtila’in , a yanzu haka  Majalisar Dinkin Duniya na fafutukar samar da matsuguni na gaggawa da kuma kayan agajin abinci. Yunkurin ceto na fuskantar cikas sakamakon ruwan sama mai yawa da kuma karancin kayan aiki.

Rahoton ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce a cikin shekaru goma da suka gabata sama da mutane dub 7,000 ne suka mutu sakamakon girgizar kasa a kasar.

 

More from Labarai