On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Taraiyy Zata Cire Tallafin Mai Daga Watan Yunin Badi

MINISTAR KUDI ZAINAB SHAMSUNA

Ministar Kudi, Kasafi da kuma tsare-tsaren cigaban kasa, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna, Ta ce, Gwamnatin taraiyya zata cire tallafin mai daga watan Yunin Badi.

Ministar ta baiyana haka ne a Abuja, a yayin wani taron manema Labarai, jim kadan bayan kammala taron bunkasa tattalin arzikin kasa karo na 28.

Idan ba’a manta ba, yawan kudin da aka biya da sunan tallafin mai daga  watan janairun shekarar da muke ciki zuwa watan Augusta, Ya kai tiriliyan 2 da bilyan 565, Haka zalika, gwamnatin taraiyyar zata kashe  zunzurutun kudi har naira tirilyan 3 da bilyan 300  daga  farkon watan  janairun sabuwar shekara mai kamawa zuwa  watan yunin shekarar, da za’a daina biyan tallafin man.

Duk da cewar cire tallafin man na daga cikin  tsare-tsaren kasafin kudi na gwamnatin taraiyya, to sai dai ministar ta baiyana cewa, babban kalubalen shine, yadda  za’a yi domin cire  tallafin na mai.

 

 

 

 

 

More from Labarai