On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Taraiyya Ta Janye Umarnin Sake Bude Jami'oin Ta

NUC

Gwamnatin taraiyya ta karkashin Hukumar kula da jami’oi ta kasa NUC ta janye umarnin da ta bawa shugabannin jami’oi na kasar nan akan su sake bude makarantun, biyo bayan umarnin da kotun Ma’aikata ta kasa ta bayar na janye yajin aikin.

Idan ba’a manta  ba, Ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauke dasa hannun  Daraktan kudi na hukumar Mister Sam Onazi a ranar Litinin, Hukumar kula da jami’oin ta umarce su dasu gaggauta sake bude jami’oin domin cigaba da harkokin koyo da koyarwa.

To sai dai kuma wata  takarda da aka kara fitarwa a jiya, Ta baiyana cewa an janye umarnin  da aka bayar na sake bude jami’oin.

Sanarwar mai dauke dasa hannun Mister Onazi, Yace an tsayar da umarnin farko da aka bayar, Sannan ana umartar dukkanin iyayen jami’oin da shugabannin jami’oin  dasu dan tsahirta  har zuwa lokacin da zasu samu sanarwa ta gaba.

 

More from Labarai