On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Taraiyya Tace Yarjejeniyar Dake Tsakaninta Da ASUU Bata Shafi Jami'oin Jihohi Ba.

BUHARI DA ASUU

Takun sakar dake tsakanin kugiyar malaman Jami’oi ta kasa ASUU da kuma gwamnatin taraiyya ka iya kara dagulewa, biyo bayan yadda Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta baiyana cewa yarjejeniyar dake tsakaninta da kungiyar Malaman jami’oi ta kasa, ba zata yi aiki akan jami’oin jihohi ba.

Wani kwamiti da gwamnatin taraiyya ta kafa a karkashin  uban jami’ar  Lokoja, Farfesa  Nimi Briggs , Ya bada shawarar biyan malaman jami’oin akan karin kaso  180 bisa  100, to amma  gwamnatin taraiyya tace  zata yi karin kaso 100 bisa  100 ne kawai.

Kazalika Kakakin Ma’aikatar Ilimi ta kasa, Ben Goong a  wata hira da aka yi dashi jiya Abuja, Ya baiyana cewa gwamnatin taraiyya ba zata  tsoma bakinta kan harkokin da suka  shafi  tafiyar da ilimi a matakan jihohi, kasancewar  yana  a bangaren  kebantattun abubuwa da doka  ta tsara.

A martaninsa  shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel  Osodoke , Yace dole ne duk wata yarjejeniya da suka kulla tsakaninsu da gwamnatin taraiyya ta shafi  jami’oin jihohin.

A yanzu dai a iya cewa a yanzu  an bude wani sabon babin takaddama tsakanin gwamnatin taraiyya da kuma kungiyar ASUU.